A ran 12 ga watan Mayu na shekarar 2008, an samu wata mummunar girgizar kasa mai karfin digiri 8.0 na ma'aunin Richter a lardin Sichuan dake yammacin kasar Sin. Yanzu jama'ar kasar Sin suna kokarin yin ayyukan ceto.
    A sa'i daya kuma, bi da bi ne masu sauraronmu suka aiko mana da wasiku da sakwanni da waya daga yankuna daban daban na duniya domin nuna jejeto, kuma suna son cigaba da sanin halin da ake ciki. Sabo da haka, mun kafa wannan filin musamman na taron manema labaru kan Internet. Idan kuna da tambayoyi game da wannan girgizar kasa, sai ku rubuta a yankin ba da tambayoyi, za su amsa tambayoyinku a kasa. Idan ba mu iya ba ku amsa game da tambayoyi, za mu gayyaci kwararru da masanan da su ba ku amsa, saboda haka, ku ji hakuri, idan ba ku iya samun amsa nan da nan.
    Mun gode muku da jejeto da kuka yi wa kasar Sin.
Yankin ba da tambayoyi
Yamkin amsoshi