Kiki Wang, wata basiniya mai tsara fasalin kayayyaki ce, wadda ta yi fice a Hollywood saboda kayayyaki da ta tsara sun fita daban saboda kyansu.
Tsarin fasali a jinin Kiki Wang yake. Tun tana da shekaru 4 take zane, kuma ta tsara fasalin jerin tufafi na farko ne ga ‘yar tsanarta, a lokacin da take shekaru 6. Bayan ta shiga Firamare, sha’awarta ga zane ya karu.
Kiki Wang ta ce, “Ina sha’awar zanen tufafi masu kyau na matan Sinawa na zamanin da, wadanda na gani a fina-finai da takardu. Na zana matan zamanin da daban-daban, na sanyawa kowannensu tufafi da kayayyakin kwalliya. Zanen da na yi, ya samu karbuwa tsakanin sa’annina, sai kuma wasu daga cikinsu suka fara karbarsu. Ina ganin a sannan ne na gano sha’awata ga tsara fasalin tufafi.”
A lokacin da Kiki Wang ta shiga makarantar midil, kaunarta ga zane ta karu. Ta kan zana abokan karatunta a lokacin da babu aji. Minti 3 kadai ta kan dauka wajen gama zane daya. “na yi ta zane, domin ina sha’awarsa. Yanzu, idan na kalli hotunan da na ajiye, na kan yi mamakin gano cewa wasu daga ciki zanen da na yi daga baya, sun dace da tunanina a lokacin yaranta,”cewar Wang.
Duk da cewa Kiki Wang tana bata lokaci sosai wajen yin abubuwan da take sha’awa, ba ta taba zama koma baya ba a wajen karatu. Ta samu gurbin karatu a jami’a mai daraja ta Renmin dake Beijing, inda ta samu shaidar digiri a fannin hada-hadar kudi.
Yayin da take Jami’a, ta ci gaba da yin zane da tsara fasali, kuma ta fara gyara fasalin tufafinta da ta saya. Bayan ta kammala karatu, ta kan saye yaduka ta nemi teloli su dinka mata bisa abun da ta zana. A hakan, Wang ta zama mai fidda salo a idon abokan karatunta da kawaye.
Bayan aiki na wasu ‘yan shekaru, Kiki Wang ta je Amurka, domin karatun digiri na biyu a jami’ar California. Ta fara shiga sana’ar kwalliya ne a shekarar 2015.
“A matsayin mai digiri na 2 a fannin hada-hadar kudi, a da ina aiki ne a matsayin manajar yanki na daya daga cikin kamfanoni mafiya karfi 500 a duniya. Na dade ina son yin wani abu a masana’antar kwaliyya. Amma abu ne mai wahala a samu aiki a masana’antar kwalliya idan ba ka da ilimi a bangaren. Don haka, saboda ba ni da wani horo a bangaren, sai na kafa kamfanina, sai kuma na fara tsara fasalin riguna ga taurarin fina finan Hollywood. Na yi sa’a na fara sana’ar kwalliya daga kan babbar lifayar Hollywood na Red Carpet,” cewar Wang.
Da iliminta da gogewarta kan aiki, Kiki Wang ta samu hanyoyi mabambanta wajen tunani game da fasalin kwalliya. Idan tana tsara fasalin kayayyaki, ba tufafin kadai take tunani ba, ta kan yi tunanin tasirin tambarin, da abun da yake bayyanawa da kuma muhimmancinsa.
Kiki Wang ta ce, “fasali na da ruhi. Fasalin da mutane za su so, ba batun kyansa ko rashinsa kadai ne mai muhimmanci ba, har ma da yadda zai dace da mai sanya tufafin da yadda mutane za su ji a zuciyarsa.”
Kafin barkewar annobar COVID-19, Wang ta kan zo kasar Sin akai-akai domin musaya da tuntubar takwarorinta ta hanyar shiga harkoki daban-daban, kamar shiga bukukuwan fina-finai da gabatar da lakca da dai sauransu.
“Na ci gajiyar tasirin al’adun Sinawa, don haka hakki na ne in yayata al’adun Sinawa ga duniya. Kwalliya ta duniya da kanta, wani tsari ne na gado, da kirkire-kirkire da dunkulewa. Ina fatan bada gudunmuwa ga dunkulewar tsarin kwalliya irin na kasar Sin da yammacin duniya ta hanyar ayyukana,” cewar Wang.
Bisa wannan tunani ne ta kirkiro jerin kayayyakin da ake kira da East Meets West, wato haduwar gabashi da yammacin duniya. Ta yi amfani da salon Sinawa da ya hada da dabbobin Loong da tsuntsayen Phoenix da furanni da makarin fuska irin na Peking Opera a fasalin kayayyakinta. Tana kuma amfani da salon surfani na gargajiya domin hada su da irin na yammacin duniya.
Jerin kayayyakinta da ake kira Nujun, ya ja hankali a masana’antar kwalliyya ta duniya kuma ya samu hawa bangon mujallu a kasashe da dama da ma liyafar Hollywood. A don haka, kafafen yada labarai na kasa da kasa ke kiran Kiki Wang da Jakadiyar kwalliya da ta hada gabashi da yammacin duniya.
“Wannan jerin wani salo ne da ya hada al’adun gabashi da yammacin duniya. Dukkan salon kwalliya na gargajiya alama ce ta tarihi, kuma akwai bukatar kare su da yayata su. Nagartattun tsarin kwalliya na Sinawa na shekaru 5,000 da suka gabata, na da daraja matuka. A matsayin Sinawa masu tsara fasalin kayyaki, muna da hakkin gado da yayata shi. Domin tsarin kwalliyar Sinawa ya samu karbuwa da masoya a duniya, muna bukatar yayata su ta hanyoyi daban-daban,” cewar Kiki Wang. Tana fatan za ta kara bada gudunmuwa wajen yayata musayar al’adu tsakanin gabashi da yammacin duniya ta hanyar tsarin fasalinta na kwalliya.(Kande Gao)