Tufafi masu launin ja na Sinawa sun samu karbuwa a Hollywood

CRI2022-02-14 19:44:32

Tufafi masu launin ja na Sinawa sun samu karbuwa a Hollywood_fororder_Kiki Wang2

Kiki Wang ta kasance babbar mai tsara fasalin kayayyaki da ta samu lambobin yabo, wadda kuma ta yi fice saboda tsara kayyaki da take yi da suka fita daban saboda kyansu. Ta kan tsarawa taurari da sanannun mutane tufafi a fadin duniya, kuma mujallu da dama sun yi hira da ita, har ma da kafafen yada labarai na kasa da kasa, game da dimbin nasarorin da ta samu a masana’antar kwalliya.

A shekarar 2020, Bvlgari, daya daga cikin manyan tambura na Italiya, ya fitar da wasu sabbin kayayyaki. Daya daga cikin tufafin dake kan gaba, Kiki Wang ce ta tsara fasalinsa. Rigar da launin ja ta mamaye, an yi masa ado da wasu launukan ruwan zinare, ta samu yabo da dama daga masana’antar. Wannan ne karon farko da Bvlgari ya hada hannu da mai tsarin fasali na kasar Sin.

Haka kuma, Kiki Wang ita ce Basiniyar dake zaune a Amurka, da ta tsara tufafi ga Miss Marvel, wadda ita ce sabuwar fuskar shirin nan mai dogon zango na Marvel Superhero. Yayin wani taron fina-finai a birnin New York a shekarar 2019, Miss Marvel ta burge mutane da jar rigarta mai matukar kyau da ke da kwalliyar ruwan zinare. An ce minti 5 kadai ya dauki Kiki Wang wajen zana fasalin tufafin.

 Tufafi masu launin ja na Sinawa sun samu karbuwa a Hollywood_fororder_Kiki Wang1

A shekarun da suka gabata, Kiki Wang ta tsara tufafin manyan bukukuwa ga taurarin Hollywood da suka taka rawa a manyan fina-finan da suka samu lambobin yabo, kamar fim din Black Panther. Galibin masu shirye-shirye da taurarin fina finai da masu tallar tufafi har ma da iyalan gidan sarautar Birtaniya, na kaunar Kiki Wang da kayayyakin da take tsarawa.

Kiki Wang ta ce, “Ni ce babbar mai tsara kayayyaki a kamfanin Kiki Wang. Burina shi ne, masu sanya tufafin da na tsara su fita daban saboda kyan fasalin tufafinsu. Tufafi na gani na fada da aka harhada abubuwa daban-daban, shi ne ma’anar kwalliya a wurina. Daga lokaci zuwa lokaci, ina son daukar wata sabuwar dabara, in zama jaruma a fagen kwalliya. Masu sayen kayayyakina sun sha fada min cewa, suna jin dadi idan suka sanya tufafin da na tsara. Ina son amfani da tsarin fasalina wajen taimakawa mutane fahimtar kansu, su kara samun kwarin gwiwa da karfi. Na kan ce tufafi, ita ce hanya mafi sauki na samun kwarin gwiwa, kuma na yi matukar sa’a ina iya cimma wannan.”

Domin tabbatar da ingancin tambarin, Kiki Wang kan yi amfani da Siliki da wasu yaduka na asali. “Ina son yaduka na asali daga halitta. Ina tunanin sun fi kare lafiya da inganci. Ingancin yadi zai sa ka ji kana da muhimmanci da kwarin gwiwa. Kuma ina son gwada sabbin kirkire-kirkire, kamar yadukan da aka yi amfani da fasaha wajen samar da su. Ina son hada abubuwa da dama domin samar da wani sabon abu na ba zata. Mun yi sa’a muna cikin wani zamanin da fasaha ke saurin bunkasa. Ana samun yaduka da dama da suka dace da kare muhalli a kullum, wannan shi ne abun da muke son mu lalubo…kirkire-kirkire a nan gaba,” cewarta.

Tsarin tufafinta masu kyau sun samu shiga manyan-manyan bukukuwa da liyafa na duniya. Kiki Wang ta gabatar da tufafinta a gomman shirye-shiryen kwalliya a kasar Sin da Italiya da Faransa da Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa. Kuma ko wanne daga cikinsu ya ja hankalin mutane kuma ya samu yabo daga kafafen yada labarai.

Tufafi masu launin ja na Sinawa sun samu karbuwa a Hollywood_fororder_Kiki Wang3

Irin kokarin Wang, ya samu yabo sosai a masana’antar kwalliya ta kasa da kasa. Ta Lashe lambobin Yabo a ciki da wajen kasar Sin, ciki har da na ’yar kasuwa da ta yi fice da kuma wadda ta tsara tufafin da ya fi kowanne na shekara, a Hollywood.

Wang da tufafin da ta tsara sun hau bangon jaridun kwalliya daban-daban. Jaridar Birtaniya CVH First Class, ta nada ta matsayin Sarauniyar tsara tufafi, kuma ta haska a mujallar Hollywood a Amurka, sun kira ta da kwararriyar ‘yar Asiya da ta yi fice a Amurka.

A baya-bayan nan, Kiki Wang ta fitar da wani jerin kayayyaki, mai suna Red Universe, domin gabatar da kwalliya ga mutane. “Ina ganin cewa, a matsayin masu tsara tufafi, aikinmu shi ne kirkirar fasaha, kuma a yi amfani da su wajen haska mutane a rayuwarsu ta yau da kullum. Na ma kirkiro wani jerin tufafi mai launin ja wato Taiduhongpin, domin cimma wannan burin. Launin ja na nufin alheri bisa al’adar gargajiya ta Sinawa, kuma ina son amfani da fasali mai launin ja don samar da farin ciki da fatan alheri ga mutanen da suka sanya tufafinm,” cewarta.

Not Found!(404)