MDD ta bukaci a kare hakkokin da suka shafi lafiyar haihuwa

CRI2021-07-12 13:04:00

MDD ta bukaci a kare hakkokin da suka shafi lafiyar haihuwa_fororder_生殖健康

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kare hakkokin da suka shafi lafiyar haihuwa, yayin da ake bikin ranar yawan jama’a ta duniya dake gudana a ranar 11 ga watan Yulin kowacce shekara.

A sakonsa domin ranar, Antonio Guterres, ya ce ya kamata a yi alkawarin tabbatar da kare hakkokin lafiyar haihuwa na dukkan mutane a kuma ko ina.

Kididdiga ta baya-bayan nan ta nuna cewa, COVID-19 zai ingiza mata da ‘yan mata miliyan 47 cikin matsanancin talauci. Kuma ba lallai ne galibin ‘yan matan da suka bar karatu su koma makaranta ba.

Ya ce a kowacce kusurwa ta duniya, ana ganin koma bayan nasarorin da aka sha wahala wajen samunsu da tabarbarewar hakkokin mata da irin zabin da suke da shi. Bayan barkewar annobar COVID-19 kuma, an karkatar da albarkatun da aka ware saboda hidimomin lafiya da suka shafi jima’i da haihuwa. Yana mai cewa ba zai yiwu a bar mata su kadai cikin wannan yaki ba.

Ranar 11 ga watan Yulin, rana ce da aka ware a matsayin ta yawan al’umma, wadda ke da nufin wayar da kan jama’a kan batutuwan da suka shafi adadinsu. (Fa’iza Mustapha)

Not Found!(404)