Jami’i a hukumar lafiyar kasar Sin (NHC) Xu Shuqiang, ya bayyana kudurin kasar Sin na gina tsarin kiwon lafiya na bai daya, mai isassun alkarkatu da zai iya samar da hidimomi masu inganci, da iya kula da kayayyakin kiwon lafiya.
Xu Shuqiang ya bayyana hake ne, yayin wani taron manema labarai da hukumar ta shirya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Ya ce, daga wannan shekara, za a mayar da hankali wajen kara karfin matakan kandagarkin lafiya da jinyar al’umma, da samar da kayayyakin aiki na zamani a asibitocin gwamnati, da inganta hidimomi na lafiya da ake baiwa wani muhimmin rukuni na al’umma, da bunkasa yadda ake gado da kirkire-kirkire a fannin magungunan gargajiyar kasar Sin.
A nasa jawabin mataimakin shugaban hukumar lafiya ta kasar Sin Li Bin, ya bayyana cewa, muddin ana son kara bunkasa gyare-gyare a fannin lafiya, akwai bukatar daidaita albarkatu a fannin kiwon lafiya da inganta tsarin yadda ake binciken cututtuka da jinyar marasa lafiya.
Wang Guodong, wani jami’i a hukumar kula da tsarin kiwon lafiya ta kasa, cewa ya yi, za a zurfafa gyare-gyare kan tsarin kula da magunguna na bai daya, inda za a kara sanya wasu nau’o’in magunguna a cikin tsare-tsaren, don rage matsin da jama’a ke fuskanta, bisa la’akari da ‘yar ribar da kamfanoni za su samu.(Ibrahim)