Jami’an aikin ceto suna ci gaba da ayyukan lalibo mutane 20 da har yanzu ba a ji duriyarsu ba bayan iftila’in zaftarewar laka wanda ta faru a sanadiyyar mamakon ruwan sama a kudu maso yammacin birnin Tokyo a tsakiyar kasar Japan.
Bala’in yayi sanadiyyar rayukan mutane biyu kana ya shafi gidaje 130, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.
Kimanin ‘yan sanda 700 da dakarun tsaro gami da jami’an kashe gobara ne suke gudanar da aikin ceton a birnin Atami, dake shiyyar Shizuoka.
Bala’in yayi sanadiyyar lalata wasu gidaje bayan da laka ta rufto kansu daga kololuwar wani tsauni da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Asabar agogon kasar, wacce tayi tafiyar nisan kilomita kusan biyu.
An fara gudanar da aikin kwashe lakar da buraguzan da suka watsu ta hanyar amfani da manyan motoci da safiyar ranar Lahadi yayin da aka samu tsakaitawar ruwan saman sai dai akwai fargabar yiwuwar sake fuskantar bala’in a karo na biyu.
An tsinci matan biyu wadanda ba su iya ko da motsi, kana daga bisani an tabbatar da mutuwarsu a ranar Asabar, dakarun tsaron tekun suna ci gaba da aikin lalibo mutanen da suka bace.
Hukumar hasashen ruwan sama ta kasar Japan ta yi gargadin samun ruwan sama kamar da bakin kwarya inda ta gargadi jama’a da su zauna cikin shiri na yiwuwar sake fuskantar zaftarewar lakar, da ambaliyar ruwa, da kuma tumbatsar teku.(Ahmad)