Masu ayyukan sama jannatin kasar Sin, Liu Boming da Tang Hongbo, sun fita daga cikin tashar sararin samaniya a kumbonsu na Tianhe da misalin karfe 11:02 na safe a gogon Beijing a yau Lahadi, inda suka fara gudanar da wasu ayyukan a wajen kumbonsu, kamar yadda hukumar dake kula da ayyukan sararin samaniyar Sin CMSA ta sanar.
Liu Boming, ya bude kofar kumbon na Tianhe tun da misalin karfe 8:11 na safe, a cewar hukumar CMSA.
Yayin fara sabbin ayyukan ‘yan sama jannatin a wani sashe na yankin tashar sararin samaniyar wato EMU, hakan na nufin ‘yan sama jannatin biyu sanye da tufafin ayyukan sararin samaniya kirar kasar Sin wato Feitian, ma’ana suna yawo a sararin samaniyar, kawo yanzu, sun riga sun kammala wasu ayyuka na daban a bangaren wasu na’urori, kamar yadda hukumar CMSA ta bayyana.
Haka zalika sun kammala ayyukan daukar kyamarorin daukar hotuna da misalin karfe 12:09 na rana.
Hukumar tace ‘yan sama jannatin zasu cigaba da gudanar da ayyuka tare domin sanya wasu muhimman na’urori tare da taimakon bangaren wasu injina.(Ahmad)