A yau Alhamis, an kaddamar da bikin murnar cikar shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), a filin Tian’anmen dake birnin Beijing na kasar. Babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin aikin soja na tsakiya na JKS, ya halarci bikin, inda zai gabatar da wani muhimmin jawabi.
Gaba daya mutane fiye da dubu 70 sun halarci gagarumin bikin na yau. (Bello Wang)