A jiya Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga shugaban kasar Zambia Edgar Lungu, bisa rasuwar tsohon shugaban kasar Kenneth Kaunda.
Cikin sakon na sa, shugaba Xi ya ce Mr. Kaunda, shahararren jagora ne wajen neman ‘yancin nahiyar Afirka, kana shi ne wanda ya kafa tushen huldar diflomasiyya tsakanin Zambia da Sin. Kaza lika a cewar shugaba Xi, marigayi Kaunda ya aiwatar da matakan karfafa hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, ya kuma kulla abota mai karfi da shugabannin Sin. Don haka Sinawa ba za su taba mantawa da gagarumar gudummawa da ya bayar ba, a fannin bunkasa alakar kasashen biyu.
Daga nan sai shugaban na Sin ya jaddada aniyarsa, ta ci gaba da aiki tare da shugaba Edgar Lungu, ta yadda za su kai ga zurfafa dankon zumunci tsakanin Sin da Zambia, tare da fadada hadin gwiwar su a dukkanin fannoni, ta yadda hakan zai haifar da gajiya ga kasashen biyu da ma al’ummun su. (Saminu)