Hassan Sani Abubakar, mazaunin Hotoro ne dake karamar hukumar Nassarawa a jihar Kanon tarayyar Najeriya, wanda ya yi shekara kusan uku yana karatu a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kasar Sin.
A zantawarsa da Murtala Zhang, Hassan Abubakar ya bayyana takaitaccen tarihinsa, gami da abun da ya ba shi karfin gwiwar zuwa karatu a kasar ta Sin. Haka kuma a cewarsa, ganin yadda kasar Sin ta samu ci gaba a fannin kimiyya da fasaha da sauransu, akwai abubuwa da dama da ya dace a koya daga kasar.
Hassan Abubakar ya kara da cewa yana jin dadin rayuwa a Chengdu, musamman a fannin ibada, bai taba gamuwa da kalubale ko tsangwama a fannin ba.
A karshe, Hassan ya baiwa matasan Najeriya kwarin-gwiwar neman zarafin karo ilimi a kasar Sin, don bada gudummawar su ga raya kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu. (Murtala Zhang)