Matakan yaki da COVID-19 na kasar Sin sun haifar da dan mai ido wajen karfafa yawon bude ido a karkara

cri2021-05-14 18:52:43

Matakan yaki da COVID-19 na kasar Sin sun haifar da dan mai ido wajen karfafa yawon bude ido a karkara_fororder_1

A kwanan nan, kafar watsa labarai ta CNN dake Amurka, ta bayyana yadda fannin yawon shakatawa a yankunan karkarar kasar Sin ke kara samun tagomashi, albarkacin nasarar da kasar ta samu, na shawo kan yaduwar cutar COVID-19, wadda ke ci gaba da addabar sassan duniya da dama.

Kafar CNN ta kara da cewa, alkaluma daga kamfanin shirin tafiye-tafiye na Trip.com, sun nuna zuwa watan Maris na shekarar nan ta 2021, adadin masu zuwa yankuna daban daban na karkarar kasar Sin, domin yawon bude ido ya karu da kaso sama da 300 bisa dari a duk shekara.

Yanzu haka dai, masu yawon shakatawa na cikin gidan kasar Sin na kara nuna sha’awa ga yawon bude ido a yankunan karkarar kasar. Wato maimakon zuwa wuraren tarihi, da gine-ginen adana su. Karkashin wannan sabon salo, Sinawa da dama na samun nishadi ta hanyar alal misali ziyartar gonaki domin tsinkar furanni ko ’ya’yan itatuwa, da kallon yadda ake shuka tsirrai, ko yadda ake kamun kifi, ko dandana nau’o’in abincin gargajiya da ake sarrafawa a yankunan karkara, a matsayin wani sabon salo na yawon bude ido.

Masharhanta da dama na alakanta wannan ci gaba da ake samu, a fannin yawon bude ido a kasar Sin, da yadda kasar ta cimma nasarar dakile yaduwar cutar COVID-19 a cikin gida, domin kuwa idan ba don an kai ga cimma wannan nasara ba, sashen bude ido ba zai samu tagomashin da yake samu a yanzu ba.

Da ma dai tuni gwamnatin kasar Sin ta sanya batun raya yankunan karkara da kawar da fatara, cikin manyan kudurorinta na bunkasa kasa. Karkashin wannan manufa, gwamnatin Sin na taimakawa matalauta dake zaune a yankunan karkara, da hanyoyin raya sana’o’i na yaki da fatara.

Baya ga horaswa a fannin sanin makamar aiki, da samar da lamunin kudade na raya sana’o’i, gwamnati na kuma gudanar da manyan ayyukan more rayuwa dake samar da ayyukan yi, da ba da damar kewayawar kudade tsakanin al’umma.

Ko shakka babu, wadannan matakai sun share fagen kyautata rayuwar mazauna yankunan karkarar kasar Sin, sun kuma ingiza ci gaban yawon bude ido mai nasaba da kauyuka a kasar Sin. Amma fa irin ci gaban da ake gani a baya bayan nan a wannan fanni, yana da alaka ta kai tsaye, da nasarar Sin ta shawo kan cutar COVID-19 a cikin gida. (Saminu Hassan)

404 Not Found

404 Not Found


nginx