Kasar Sin tana goyon-bayan WTO wajen gudanar da shawarwari kan shirin dakatar da ‘yancin mallakar fasahar kera alluran rigakafin cutar COVID-19

CRI2021-05-13 21:03:31

Kasar Sin tana goyon-bayan WTO wajen gudanar da shawarwari kan shirin dakatar da ‘yancin mallakar fasahar kera alluran rigakafin cutar COVID-19_fororder_2bd9-kpzzqmz6182891

Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng, ya bayyana a yau Alhamis cewa, Sin ita ce kasa ta farko da ta mayar da alluran rigakafin cutar COVID-19 a matsayin wani kayan amfanin al’ummar duk duniya. A halin yanzu kuma, kasashe membobin hukumar kasuwancin duniya wato WTO, suna tattaunawa kan yadda za’a yi don kowa da kowa ya amfani alluran rigakafin.

Gao Feng ya yi karin haske da cewa, kasar Sin tana ganin cewa, WTO na iya taka muhimmiyar rawa a wannan fanni. Kana Sin tana marawa WTO baya wajen shiga matakin tattaunawa, kan shirin dakatar da ‘yancin mallakar fasahar kera alluran rigakafin cutar COVID-19. A nan gaba kuma, Sin za ta yi kokari tare da bangarori daban-daban, don taimakawa ga cimma nasarar shiri mai amfani da adalci, ta yadda kasashen duniya za su iya samun nasarar dakile cutar cikin gaggawa. (Murtala Zhang)

404 Not Found

404 Not Found


nginx/1.26.1