Wasan ‘yar igiya mai hade da rawar titi ta zamani yana samun shahara a tsakanin matasan kasar Sin

CRI2021-05-13 15:42:42

Wasan ‘yar igiya mai hade da rawar titi ta zamani yana samun shahara a tsakanin matasan kasar Sin_fororder_个人1.JPG

Wasan tsallake igiya wato ‘yar igiya, na da tarihi fiye da shekaru dubu 1 a kasar Sin. Tun daga kananan yara zuwa tsofaffi, dukkansu suna son irin wannan wasa. A ganin Sinawa, wasan ‘yar igiya wasan gargajiya ne, yawancinsu sun maida wasan a matsayin hanyar motsa jiki kawai, amma akwai wasu mutane da ke sabunta fasahohinsa, da maida shi matsayin wata hanyar yin mu’amalar al’adu.

Wu Wangqiang, wanda ya taba samun lambar yabo ta wasan ‘yar igiya ta duniya, ya riga ya yi aikin yada wasan ‘yar igiya har na tsawon shekaru fiye da 10. Tun daga lokacin da yake karatu a jami’a, har zuwa zamansa mai horaswa a yanzu, ya ci gaba da yin kokarin yada wasan ‘yar igiya.

Bayan da ya shiga jami’ar wasannin motsa jiki ta Shanghai, Wu Wangqiang ya gano wata kungiyar wasan ‘yar igiya a cikin jami’a, ya ga shirin nuna fasahar wasan ‘yar igiya da memebobin kungiyar suke yi, wanda ya burge shi kwarai. Ya nuna sha’awar wasan, tun daga wancan lokaci, ya fara koyon wasan ‘yar igiya mai fasaha ta musamman. Ya ce, wannan fasaha, bai taba ganin ta kafin lokacin ba. Ya ce,“Yawancin mutane suna maida wasan ‘yar igiya a matsayin hanyar gargajiya ta wasan motsa jiki. Ban taba tunin za a iya hada shi da rawar titi, ko fasahohin lankwasa jiki ba, har ma a yi alkahura a yayin wasan ‘yar igiya, hakan ya burge ni sosai.”

Domin kaunar wasan, Wu Wangqiang ya kiyaye yin kokari koyon fasahohin wasan tare da abokan karatunsa a jami’a. A shekarar 2014 da kuma 2015, ya samu damar halartar gasar wasan ‘yar igiya ta duniya, saidai ya gano ‘yan wasan daga kasashen Japan, da Amurka suna da kwarewa kan wasan, don haka ya yi tunani cewa, idan an iya shigar da wasu kide-kide ko raye-raye a cikin wasan, hakan zai sa mutane su kara nuna sha’awar wasan, da kara son kallon sa.

Lokacin da yake koyar da wasan ga kananan yara, ya gano idan aka saka kide-kide da raye-raye a cikin wasan, hakan na sa yaran sun fi son yin wasan, da kara jin dadin sa.

Wasan ‘yar igiya mai hade da rawar titi ta zamani yana samun shahara a tsakanin matasan kasar Sin_fororder_16年夺冠颁奖照片.JPG

A shekarar 2016, shi da tawagarsa, sun halarci gasar wasan ‘yar igiya ta duniya a kasar Portugal, inda ya shigar da kidan al’adun gargajiya na kasar Sin, da wasu abubuwan dake shafar al’adun gargajiya na kasar Sin a yayin gasar. Wannan ne karo na farko da aka shigar da irin wadannan abubuwa masu alaka da al’adun gargajiya na kasar Sin a cikin wasan, kuma shi da tawagarsa sun cimma nasara a wasan ‘yar igiya masu hade da fasahohi na musamman a yayin gasar.

A ganin Wu Wangqiang, ana iya shigar da abubuwa daban daban a yayin wasan ‘yar igiya, ana kuma iya yin kirkire-kirkire a wasan. Ya ce,“Wasan ‘yar igiya wasa ne mai iya hade abubuwa daban daban, kamar su rawar titi, ko wasu al’adun gargajiya na Sin da sauransu. Akwai wasu ‘yan wasan rawar motsa jiki don kara lafiya da suke shigar rawar motsa jiki a wasan ‘yar igiya, kana wasu ‘yan wasan ‘yar igiya daga yankin arewa maso gabashin kasar Sin, suna shigar da rawar yankinsu a wasan, wadanda duk suna da ban sha’awa sosai.”

Wu Wangqiang ya ce, wasan ‘yar igiya wasa ne na gargajiya na al’ummar kasar Sin, saka sabbin abubuwa a wasan ya sa kaimi ga mutane su kara karbar wasan cikin sauki, su san wasan ‘yar igiya da aka fito shi a kasar Sin, ya kuma iya samun karbuwa sosai a tsakanin jama’a, musamman matasa ta yadda za su kara nuna sha’awar wasan.

Da yake matasa ba su ciki son wasan ba, amma idan aka saka sabbin hanyoyin yin wasan, kamar rawar titi da sauran hanyoyi masu dacewa da zamani, wadanda suka jawo hankalin matasa sosai, kuma matasa na son shaida kwarewar musamman tasu ga saura, hakan ai sa wasan ya samar musu damar yin kirkire-kirkire, da jawo hankalin saura sosai.

Wasan ‘yar igiya mai hade da rawar titi ta zamani yana samun shahara a tsakanin matasan kasar Sin_fororder_17年美国世锦赛-交互绳项目照片.JPG

Game da zama zakara na duniya, Wu Wangqiang ya ce bayan da ya samu lambar yabo, da farko ya yi farin ciki sosai, da murnar kwarewar sa a wasan, amma daga baya ya waiwayi fasahohi, ya san akwai babban gibi a tsakanin sa da kwararrun wasan na duniya. Don haka, ya ce ya jingine nasarar da ya yi a baya, zai kuma ci gaba da yin kokari. Yana fatan more fasahohinsa, da sauran masu koyo ko sha’awar wasan, da samar da gudummawarsa wajen yada wasan a kasar Sin, har ma a dukkan duniya baki daya.

Wu Wangqiang ya ce, yanzu wasan ‘yar igiya ya kasance wani muhimmin kashi a rayuwarsa, wanda ke da nasaba da aikinsa, da sauran harkokin rayuwarsa, ta yadda ba zai iya raba wasan da rayuwarsa ba. Ya ce,“A gani na na yi sa’a. A zamanin yanzu, na iya maida abin da nake sha’awa da kwarewa ya zama aikina. Don haka, ina son ci gaba da yin kokari, da kara samar da gudummawa wajen yada wasan ‘yar igiya.”

Cutar COVID-19 ta bazu a kasar Sin a shekarar 2020, an kuma dakatar da dukkan kos na kamfaninsu. Sai dai shi da abokan aikinsa sun nemi sabbin hanyoyin yada wasan ‘yar igiya, kuma ya bude shafin internet nasa, a kan manhajar TikTok, don gwada shirin koyar da wasan, da gabatar da shirin wasansa dake hada da rawar titi ta yanar gizo.

Da farko, bai tunanin hakan zai iya samun karbuwa ba, yanzu ya samu masu bin shafin na sa su fiye da dubu 140 a Tik Tok. Ko da yake ba shi da wata sha’awar kasance mutum mai samun karbuwa sosai, a ganinsa wannan ce sabuwar hanyar yada wasan ‘yar igiya. Ya ce,“Na taba shiga wata makaranta ta koyar da wasan ‘yar igiya. Idan akwai dalibai dari biyar a makarantar, toh su duka dari biyar din za su san wasanmu na ‘yar igiya mai fasaha ta musamman. Idan kuwa muka tsara bidiyo game da wasan, muka gabatar da su a internet, hakan zai sa kaimi ga yada wasanmu na ‘yar igiya cikin sauri. Muna son yin amfani da wannan sabuwar hanya mai dacewa da yanayin yanzu, don sa kaimi ga yada wasan ‘yar igiya yadda ya kamata.”

Game da halartar gasannin wasan ‘yar igiya na kasa da kasa, Wu Wangqiang ya ce ya fuskanci kalubale da mawuyacin hali. Da farko, idan ya tafi kasashen waje don halartar gasar wasan, yana tuntubi masu shirya gasar da kansa, ya sayen tikitin jiragen sama da kansa, da daidaita dukkan matsaloli da kansa. A lokacin, iyalansa da abokan aikinsa da kuma shugaban kamfaninsa sun nuna goyon baya gare shi sosai.

Da farko, iyayen Wu suna fatan zai samu aikin malanta, ko aikin hukuma ko gwamnati, amma sun ga Wu ya yi kokari sosai a fannin wasan ‘yar igiya, don haka sai suka nuna goyon baya gare shi. Mamarsa ta ce,“Wasan ‘yar igiya da Wu ke sha’awa shi ne kuma aikinsa, abin sha’awarsa ya zama aikinsa, mu iyaye muna nuna goyon baya gare shi.”

A yayin da Wu yake koyon wasan ‘yar igiya mai fasaha ta musamman, akwai kungiyar wasan kawai a jami’a, wadda ke koyar da fasahohin wasan. Amma yanzu, an kafa fannin karatu na koyar da wasan ‘yar igiya a jami’ar wasannin motsa jiki ta Shanghai. Xu Faguang, abokin aiki ne na Wu ne, shi ma ya gama karatu a jami’ar Wu, ya ce,“A lokacin da malam Wu ke karatu, akwai kungiya da ke koyar da fasahohin wasan ‘yar igiya. Kana a lokacin da nake karatu a jami’a, an kafa fannin karatu na musamman na koyar da wasan, don haka na yi karatu a fannin. Na yi karatu kan wasan, na samu horo, da kuma halartar gasannin wasan, kuma a lokacin ne na gamu da Wu na kuma shiga tawagarsa.”

Wasan ‘yar igiya mai hade da rawar titi ta zamani yana samun shahara a tsakanin matasan kasar Sin_fororder_微信图片_20210512085026

Ban da yada wasan a kasar Sin, Wu da tawagarsa suna kokarin more fasahohinsu da sauran kungiyoyin wasan daga sassan daban daban na duniya, ciki har da tarayyar Nijeriya. A shekarar 2018, kungiyar kawancen wasan ‘yar igiya ta Nijeriya, ta tura wata tawaga zuwa birnin Shanghai, don yin mu’amala da musayar fasahohi a tsakaninta da tawagar Wu. Koda yake tawagar Wu ta taba yin mu’amala da kungiyar nahiyar Afirka daya ce kacal, amma kamfaninsa wato Yuedong yana son ci gaba da yin mu’amalar fasahohin wasan ‘yar igiya a tsakaninsa da kungiyoyin Afirka. Manejan kamfanin Yuedong Zhong Shuijun ya bayyana cewa,“Jikin ‘yan Afirka yana da karfi sosai, muna son kara yin mu’amala tare da sauran kasashen waje, musamman kasashen Afirka. Yanzu masu yin wasan a Afirka ba su da yawa, don haka akwai damar bunkasa wasan a nahiyar.”

Game da burinsa, ya ce dukkan ‘yan wasan ‘yar igiya suna fatan wasan zai shiga gasar wasannin Olympics. Zai kuma kara samun kirkire-kirkire, ya ce,“Za mu yi amfani da hanyoyi iri daban daban, don jawo hankalin masu sha’awar wasan ‘yar igiya. Ban da rawar titi da Kungfu, za mu yi amfani da kwarewarmu, wajen yin kirkire-kirkire. Muna fatan duniya za ta ga kwarewa da fasahar wasan na kasar Sin.”(Zainab)

Not Found!(404)