Kwanan baya, darakta janar na hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya sanar da cewa, an shigar da alluran riga kafin COVID-19 kirar kamfanin Sinopharm na kasar Sin, a cikin jerin sunayen riga kafin da ake iya amfani da su a matakin gaggawa.
Da haka, rigakafin na kamfanin Sinopharm sun zama na farko baya ga na yammacin duniya a jerin sunayen wadanda WHOn ta amince da su, kuma wannan ne karo na farko da allurar rigakafin cututtukan dake yaduwa samfurin kasar Sin, ta samu izinin amfanin gaggawa daga WHO.
Game da hakan, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kokari tare da kasashen duniya, don inganta samun damar yin riga kafi cikin adalci tsakanin kasashe masu tasowa, da ba da gudummawa ga cimma nasarar yaki da annobar a duniya. (Bilkisu)