A jiya Alhamis, daraktar shiyyar Afirka ta hukumar lafiya ta duniya WHO Matshidiso Moeti, ta shaidawa taron masu ruwa da tsaki na mako mako ta kafar bidiyo cewa, jinkirin samar da isassun alluran rigakafin cutar numfashi ta COVID-19, da kalubalen bullar sabbin nau’o’in cutar a wasu sassa, na barazana ga nasarar shawo kan cutar a nahiyar Afirka.
Moeti ta kara da cewa, tsanantar yanayin yaduwar wannan annoba a Indiya, na cikin manyan dalilan da suka haifar da tsaikon samun karin rigakafi ga nahiyar. Kuma akwai fargabar sake bullar cutar a wasu sassan nahiyar sakamakon wannan matsala.
Cikin wata sanarwa da ofishin ta ya fitar kuwa, Moeti ta ce, "Yayin da muke kira da a samu daidaito wajen raba rigakafin, ya zama wajibi nahiyar Afirka ta zage damtse wajen yin cikakken amfani da rigakafin da ke hannun ta. Dole ne a yiwa al’umma dukkanin alluran da a yanzu suke hannu”.
Moeti ta kara da cewa, bisa kididdiga, mutum 8 cikin duk mutum 1000 ne suka samu rigakafin a Afirka, sabanin sauran sassan duniya da adadin ya kai mutum 150 cikin duk mutum 1,000, wanda hakan alama ce ta rashin kyawun yanayin rigakafin a nahiyar.
Kaza lika, alkaluman cibiyar Afirka CDC sun nuna cewa, al’ummun nahiyar Afirka sun samu alluran rigakafi miliyan 37.6, yayin da ya zuwa ranar 4 ga watan nan na Mayu, aka yiwa mutane miliyan 20.2 rigakfin a nahiyar.
Afirka CDC ta kara da cewa, kasashen da ke kan gaba wajen yiwa al’ummun su rigakafin a Afirka su ne Morocco, da Najeriya, da Habasha, da Masar da kuma Kenya.
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce a halin yanzu, Afirka na da kaso 1 bisa dari ne kacal, na daukacin rigakafin da aka yi a duniya, adadin da ya ragu daga kaso 2 bisa dari da aka samu a makon da ya gabata, sakamakon karancin alluran da nahiyar ke fuskanta. (Saminu)