Mummunar gurbatacciyar iska tana illata lafiyar yawancin kananan yara a duniya

CRI2021-04-30 19:11:53

Mummunar gurbatacciyar iska tana illata lafiyar yawancin kananan yara a duniya_fororder_src=http___pic3.zhimg.com_v2-0a244217cad6bc38de590d4fea9336b5_1200x500&refer=http___pic3.zhimg

Kwanakin baya, hukumar kiwon lafiyar kasa da kasa wato WHO ta yi gargadin cewa, kananan yaran da yawansu ya wuce kaso 90 a duniya suna shakar gurbatacciyar iska, lamarin dake kawo wa lafiyarsu da ci gabansu barazana. Don haka WHO ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa.

A shekarar 2016 kadai, kananan yara dubu 600 ne suka rasa rayukansu a sanadin kamuwa da cutar numfashi mai tsanani dake shafar huhu , wadda gurbatacciyar iska ta haddasa. Akwai gurbatacciyar iska a ciki da wajen daki, don haka kananan yara a duniya, musamman ma wadanda ke zama a kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga ke kara fuskantar barazana ta fannin kiwon lafiya.

Dangane da lamarin, Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, “Gurbatacciyar iska kan illata lafiyar kananan yara. Muhimmin dalilin da ya sa haka shi ne domin sun fi baligai saurin yin numfashi, don haka sun fi shigar da gurbatacciyar iska cikin jikinsu. Ban da haka kuma, kananan yara ba su da tsayi, shi ya sa suka fi baligai kusantar doron kasa, inda akwai yawan gurbatacciyar iska, wadanda ke barazana ga lafiyar kwakwalwarsu da yadda suke girma yadda ya kamata.”

WHO ta kara da cewa, idan masu juna biyu suka shaki gurbatacciyar iska, to, mai yiwuwa su haihu kafin lokaci, kuma jarirai sabbin haihuwa su kan fuskanci matsalar rashin isasshen nauyin jiki. Har ila yau gurbatacciyar iska ta kan illata kwarewar fahimtar kananan yara, tare da haddasa asma da ciwon sankara. Ban da haka kuma, a cikin iyalan da su kan amfani da gurbataccen makamashi wajen dafa abinci, dumama daki da haskaka daki, jarirai sabbin haihuwa da kuma kananan yara su kan fuskanci barazanar lafiya sakamakon gurbatacciyar iska a cikin daki.

Sabili da haka ne WHO ta kalubalanci hukumomin lafiyar kasa da kasa da su dauki matakai, su bai wa kwararru masu ilmin lafiya bayanai, da ba su horo da albarkatu, tare kuma da shiga ayyukan tsara manufofi tsakanin mabambantan hukumomi. Ta kuma karfafa gwiwar dukkan kasashen duniya da su kai matsayin WHO dangane da ingancin iska.

Hukumar ta kuma ba da shawarar cewa, ya kamata a kyautata sarrafa shara, da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli sakamakon kona shara, a tabbatar da ganin an dafa abinci, dumama daki da haskaka daki ta hanyar amfani da fasahar zamani da makamashi masu kiyaye muhalli, a kokarin kyautata ingancin iska a gida da unguwa. (Tasallah Yuan)

—  相关新闻  —

Not Found!(404)