Ma’aikatar lafiya ta Chile ta fitar da sakamakon nazarin tasirin rigakafin kamfanin Sinovac

CRI2021-04-20 15:28:00

Ma’aikatar lafiya ta Chile ta fitar da sakamakon nazarin tasirin rigakafin kamfanin Sinovac_fororder_疫苗-3

Ma’aikatar lafiya ta kasar Chile, ta fitar da sakamakon nazarin tasirin rigakafin cutar numfashi ta COVID-19, samfurin kamfanin Sinovac Biotech na kasar Sin.

Rahoton sakamakon ya nuna yadda rigakafin ke da tasiri wajen kandagarkin harbuwa da cutar ga mutanen da aka yiwa gwaji da kaso 67 bisa dari, kwanaki 14 bayan sun karbi zagaye na biyu na rigakafin.

Kaza lika bayan karbar rigakafin da kwanaki 14, tasirin kaucewa kwantar da wadanda aka yiwa rigakafin a asibiti ya karu zuwa kaso 85 bisa dari, yayin da tasirin kaucewa rasa rayuka sakamakon cutar bayan rigakafin ya kai kaso 80 bisa dari.  (Saminu)

Not Found!(404)