Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikawa takwaransa na Jumhuriyar Demokiradiyar Congo, Denis Sassou-Nguesso, sakon taya murnar sake zabensa a matsayin shugaban Jamhuriyar Congo.
A cikin sakon nasa, Xi ya yi nuni da cewa, a cikin ‘yan shekarun nan, hadin gwiwar Sin da Jamhuriyar Congo bisa manyan tsare-tsare, ta ci gaba da bunkasa. Amincewa da juna ta fannin siyasa ya ci gaba da zurfafa, kana alakarsu a fannoni daban-daban ta haifar da sakamako mai kyau.
Shugaba Xi ya ce, yana dora muhimmanci matuka, kan alakarsu, yana kuma fatan yin aiki tare da shugaba Denis Sssaous-Nguesso, wajen zurfafa alaka a fannoni daban-daban, ta yadda hakan zai amfani kasashen biyu da ma al’ummominsu.(Ibrahim)