Jiya Laraba, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya tattauna da takwaransa na kasar Singapore Vivian Balakrishnan a birnin Nanping dake lardin Fujian.
A yayin ganawar tasu, Wang ya yiwa Vivian Balakrishnan maraba da zuwa, da ya zabi Sin ta zama kasa ta farko da ya kai ziyara, ban da kasashen ASEAN tun barkewar cutar COVID-19, abun da ya nuna cewa, huldar kasashen biyu na cikin hali mai kyau, kuma ta zama abin koyi. Bara ne, kasashen biyu, suka cika shekaru 30 da kafuwar dangantakar diplomasiyyar a tsakaninsu. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da firaminitan kasar Singapore Lee Hsien Loong ta wayar tarho, inda suka jagorancin bunkasuwar huldar kasashen biyu nan gaba, wadda ta samu ci gaba duk da barkewar mumunar cutar. A halin yanzu an samu manyan sauye-sauye a shiyya-shiyya, Sin tana fatan kara hadin kai da Singapore, don zurfafa mu’ammala da gaggauta hadin kai da ba da gudunmawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar, da kyautata tsarin gudanar da harkokin duniya, matakan da suka isar da sakwanni masu yakini ga duniya na dukufa kan shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa tare.
A nasa bangare, Vivian Balakrishnan ya taya JKS mai mulkin kasar Sin, murnar cika shekaru 100 da kafuwa, inda ya jinjinawa babban ci gaban da Sin ta samu wanda ba a taba garin irinsa ba a tarihin Bil Adam, kana ya yaba babbar nasarar da Sin ta samu wajen kawar da matsanancin fatara. Ya ca kasar Singapore na fatan inganta hadin kai da kasar Sin a duk fannoni, da ingiza bunkasuwar huldarsu. A cewarsa, kasashen biyu suna farfadowa sosai daga cutar, kuma kasarsa na maraba da shawarar da Sin ta gabatar ta amincewa da takardar shaidar lafiya tsakaninsu, ta yadda za a kyautata zirga-zirga tsakanin kasashen biyu. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun sa hannu kan yarjejeniyar huldar abota a duk fannoni ta fuskar tattalin arziki, tare da bayyana niyyarsu ta nuna adawa da manufar ba da kariyar ciniki da ingiza ciniki cikin ‘yanci da dunkulewar tattalin arzikin shiyyar waje guda. (Amina Xu)