Sin ta yi watsi da sanarwar hadin gwiwar kasashe 14 game da rahoton WHO

CRI2021-03-31 21:15:15

Kasar Sin ta yi watsi da sanarwar hadin gwiwar Amurka da wasu kasashe 13, wadda a cikin ta, hadakar kasashen suka ce wai, sun damu game da abun da yake kunshe cikin rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO, game da sakamakon binciken da aka gudanar, na gano asalin cutar COVID-19.

Da take tsokaci game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce wannan sanarwa ta nuna yadda wasu kasashe ke wulakanta kimiyya, suna siyasantar da binciken da ake yi game da asalin wannan cuta.

Hua Chunying ta yi wannan tsokaci ne, yayin da take amsa wata tambaya mai nasaba da wannan batu, yayin taron rana rana da aka saba gudanarwa, tana mai cewa, Sin ta sha nanata cewa, aikin binciken asalin kwayar cutar COVID-19 ya shafi kimiyya ne, wanda kuma ya dace masana a fannin daga dukkanin duniya su ba da gudummawar cimma nasararsa. Bai kuma kamata a siyasantar da shi ba. (Saminu)

Not Found!(404)