Wasu majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, wani harin da kungiyar BH ta kai wani kauyen yankin arewa mai nisa na Kamaru a daren ranar Asabar, ya yi sanadin mutuwar fararen hula 3 da soja 1.
Majiyoyin sun ce, mayakan dauke da manyan makamai sun shiga kauyen Dabanga na yankin ne cikin motoci da babura da dama, inda suka kone shaguna da gine-gine, tare da harbin kan mai-uwa-dawabi.
Jami’in yankin sun ce an kashe a kalla fararen hula 3 da soja 1 yayin harin. Haka kuma an kashe mayakan BH 3.
Wani soja ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, da sojoji ba su isa yankin a kan lokaci tare da mayar da martani ba, da adadin wadanda suka mutu ya zama mai matukar tayar da hankali. (Fa’iza Mustapha)