Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying, ta bayyana cewa, kasarta tana taya al’ummar Congo (Brazzaville) murnar kammala babban zaben kasar cikin lumana, tana kuma taya shugaba Denis Sassou-Nguesso, bisa sake zabarsa da aka yi. Kasar Sin ta yi imanin cewa, karkashin jagorancin shugaba Sassou, al’ummar Congo (Brazzaville) za su samu sabbin manyan nasarori a fannin bunkasa kasarsu. (Ibrahim Yaya)