A yau ne, memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Rasha Sergei Lavrov, inda ya bayyana cewa, a kwanakin baya, wasu kasashen yammacin duniya sun zargi kasar Sin ba tare da wata hujja ba, amma ya kamata su sani cewa, lokacin yin amfani da wani lamari maras tushe ko karya don tsoma baki a harkokin cikin gida na kasar Sin ya wuce.
Wang Yi ya yi nuni da cewa, a yayin taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD da ke gudana a halin yanzu, kasashe fiye da 80 sun yi jawabin nuna goyon baya ga kasar Sin kan batun jihar Xinjiang, wannan ya shaida cewa, wasu kasashen yammacin duniya ba su wakilci matsayin dukkan kasashen duniya ba. (Zainab)