Wurin shakatawa na tsaunin Xieshan na yankin Hukou dake tsakiyar tabkin Boyanghu, tsuntsaye da dama sun kaura zuwa wannan wuri a lokacin sanyi, kashinsu mai launin farin fat sun shafi itatuwa da duwatsu a tsaunin, kamar wani tsauni na kankara. Amma a wani bangare na daban kuma, babu kashin tsuntsaye. (Amina Xu)