Kasashen Afirka na ci gaba da karbar alluran riga kafi daga shirin COVAX

CRI2021-03-10 17:02:54

Kasashen Afirka na ci gaba da karbar alluran riga kafi daga shirin COVAX_fororder_微信图片_20210310170103

Yayin da kasashe masu tasowa suka fara amfani da alluran riga kafin COVID-19 karkashin shirin nan na COVAX, da ma tallafin alluran riga kafin COVID-19 daga kasashe kamar kasar Sin, akwai bukatar a yiwa amfani da wadannan allurai yadda ya kamata, a kokarin ganin bayan cutar har ma a kai ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

Kasar Ghana ce kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta fara amfana da riga kafin karkashin shirin na COVAX, inda ta karbi kimanin alluran riga kafi 600,000 na kamfanin AstraZeneca, ita ma Najeriya ta karbi kasonta na farko na alluran riga kafin COVID-19 daga shirin na COVAX, a kokarin da mahukuntan kasar ke yi na dakile wannan annoba. Ana sa ran Najeriya za ta karbi allurai miliyan 16 a rubu’i na farko na bana, yayin da aka jinkirta kason da kasar Zimbabwe za ta samu karkashin shirin na COVAX zuwa watan Mayu.

Sauran kasashen Nahiyar ta Afirka da suka karbi riga kafin na COVAX, sun hada da Uganda da Habasha da Rwanda, da Jamhuriyar demokiradiyar Congo, da Gambia, da Angola, da sauransu.

Sai dai ba a nan take ba, wai an danne Bodari a ka, duk da alluran riga kafi gami da matakan da yaki da cutar da kasashe suke dauka, akwai bukatar su ma al’umma su bayar da hadin kai ta hanyar karbar riga kafi da martaba matakan lafiya na yaki da wannan annoba. Idan kana da kyau to, ka hada da wanka.

Kamar yadda ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada yayin taron manema labaran da aka shirya a Lahadin da ya gabata a yayin taron majalisar wakilan jama’ar kasar dake gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, bai kamata kasashen duniya su riga siyasantar da hadin gwiwar samar da alluran riga kafin annobar COVID-19 ba, da ma yadda wasu kasashe ke kokarin mallake alluran riga kafin, maimakon samar da su ga kasashe mabukata, musamman kasashe masu tasowa. Domin ta haka ne kadai, za a ga bayan wannan annoba baki daya. (Ibrahim Yaya)

404 Not Found

404 Not Found


nginx