Kwararrun WHO: Binciken kwayar cutar COVID-19 a birnin Wuhan ya gudana cikin nasara

CRI2021-02-13 16:14:38

Tawagar kwararru na hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce ta gano abubuwa da dama game da asalin kwayar cutar da ta haifar da annobar COVID-19, yayin aikin da ta yi a kasar Sin a baya-bayan nan.

Shugaban tawagar Peter Ben Embarek, ya ce ziyarar tawagarsa a kasar Sin, ta gudana cikin nasara ta fuskoki da dama, inda kuma ta samu karin sabbin ilimomi game da barkewar cutar da asali da yanayi da hallayarta.

Ya jaddada cewa, babu wani dakin gwaji a Wuhan dake da kwayar cutar, kuma babu wanda ya taba ganinta kafin barkewarta.

A cewarsa, kwararrun na WHO sun ziyarta tare da tattaunawa da dakunan gwaje-gwaje daban daban dake Wuhan, kuma sun gano cewa, babu wani cikinsu dake aiki kan kwayar cutar, abun da ya yi daidai da furucin sauran dakunan gwaje-gwaje dake fadin duniya, wato babu wani dakin gwaji da ya yi aiki kan da kwayar cutar. (Fa’iza Mustapha)

404 Not Found

404 Not Found


nginx