Wasu alkaluma da hukumar kididdigar kasar Sin (NBS) ta fitar a baya-bayan nan sun nuna cewa, GDPn kasar ya karu da kaso 2.3 a shekarar 2020, bisa makamancin lokaci na bara, inda ya haura Yuan Triliyan 100, kwatankwacin dala triliyan 15.42, inda ya kai Yuan triliyan 101.5986.
Alkaluman hukumar sun nuna cewa, saurin ya zarce karuwar kaso 0.7 da aka samu a watanni tara na farkon shekara. A rubu’i na hudu na shekarar 2020 kuwa, GDPn kasar ya karu da kaso 6.5 cikin 100, idan an kwatanta da makamancin lokaci na bara, saurin fiye da kaso 4.9 na bunkasar da aka samu a rubu’i na uku na shekara.
Hukumar ta kara da cewa, harkokin tattalin arzikin kasar ya farfado yadda ya kamata, inda ayyukan yi da zamantakewar jama’a duk suka inganta. Haka kuma, an yi nasarar kammala manyan ayyukan dake shafar tattalin arziki, da jin dadin jama’a fiye da yadda aka yi hasashe.
Alkaluman hukumar sun kara nuna cewa, kasuwar aikin yi ta kasar Sin ta daidaita a shekarar ta 2020, inda bincike da aka gudanar game da rashin aikin yi a yankunan biranen kasar, ya tsaya kan kaso 5.6, kasa da abin da gwamnati ta yi fatan cimmawa a shekara, na kimanin kaso 6 cikin 100.
Babbar darektar dandalin tattalin arzikin duniya (WEF) Sa’adia Zahidi ta bayyana cewa, matakan da kasar Sin ta yi amfani da su, har suka kai ga farfadowar tattalin arzikin kasar cikin hanzari fiye da yadda aka yi zato, bayan fama da annobar COVID-19, wata alama ce mai haske wadda kuma ka iya zama abin koyi ga sauran kasashe.
Asusun IMF da sauran sassan masu zaman kansu, sun yi hasashen cewa, kasar Sin ce kasa daya tilo cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, da za ta samu karuwar bunkasuwar tattalin arziki bayan wannan annoba. (Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)