Hukumar kula da kan iyakoki ta kasar Sudan ta zargi kasar Habasha da laifin saba yarjejeniyar dake shafar kan iyakoki wanda kasashen biyu suka cimma, kamfanin dillancin labarai na SUNA ya bada rahoton.
Tun da farko a wannan rana, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta ce, wani jirgin saman sojojin Habasha ya kutsa zuwa kan iyakar kasar Sudan, lamarin da ta bayyana a matsayin mummunan matakin tsokana.(Ahmad)