Riek Machar ya bukaci a aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa da Sudan

CRI2021-01-11 11:18:47

Mataimakin shugaban kasar Sudan ta kudu na farko Riek Machar, ya yi kira da a aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa ta shekarar 2012, wadda kasarsa ta cimma da makwabciyar ta Sudan, a wani mataki na bunkasa cinikayya, da ba da damar zirga zirgar al’ummun kasashen biyu ba tare da wani tarnaki ba.

Machar wanda ya yi wannan kira a jiya Lahadi, yayin bikin bude baje kolin harkokin cinikayya tsakanin kasashen biyu a birnin Juba, ya ce yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a watan Satumbar 2012, ta baiwa al’ummun kasashen biyu damar mallakar kadarori, da zirga zirga, da zama, tare da gudanar da ayyuka a kasashen juna.

Kaza lika yarjejeniyar da aka sanyawa hannu lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Sudan Omar Al Bashir a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ta shafi harajin danyen mai, da harkokin tsaro, da na shata kan iyakokin kasashen biyu.

Baje kolin na wannan karo dai zai gudana ne har zuwa ranar 15 ga watan nan na Janairu. (Saminu) 

Not Found!(404)