Me Ya Sa 'Yan Siyasan Kasashen Yammacin Duniya Suke Mara Wa Scott Morrison Baya?

CRI2020-12-03 20:18:34

Me Ya Sa 'Yan Siyasan Kasashen Yammacin Duniya Suke Mara Wa Scott Morrison Baya?

Kwanan baya, an yi Allah wadai da babbar murya kan yadda sojojin kasar Autraliya suka kashe wadanda ba su ji ba su gani ba a kasar Afghanistan. Firaministan Australiya Scott Morrison ya ce dole ne kasar Sin ta nemi gafara daga kasarsa saboda wani zanen da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya wallafa a shafinsa na Twitter dangane da yadda sojojin Australiya suka kashe fararen hula a Afghanistan.

Abin da mista Morrison ya yi tamkar abin dariya ne. Amma wasu ’yan siyasa na kawayen Australiya da kafofin yada labaru na yammacin duniya sun tayar da jijiyar wuya, inda suka yi shelar cewa, za su hada hannu da Australiya wajen yaki da kasar Sin. To, ina dalilinsu?

Da farko suna kokarin taimaka wa Australiya ne, don ta dauke hankalin jama’a daga abin da sojojin kasar suka aikata a Afghanistan da kuma boye laifuffukan da suka aikata. Haka kuma, a matsayinsu na kawayen Australiya, Amurka da Birtaniya suna son hada kai da Australiya su nuna wa kasar Sin karfinsu, a yunkurin boye laifuffukan da suka aikata a Afghanistan da kuma bata sunansu na masu rajin kare hakkin dan Adam. Wani dalili mai muhimmanci shi ne, wasu ’yan siyasan kasashen yammacin duniya masu taurin kai wadanda suke kallon kasar Sin bisa tunaninsu, suna ganin cewa, suna da da’a, suna da ikon yanke hukunci kan wasu. Su kan soki kasar Sin da sauran kasashen duniya, amma ba su son kasar Sin da sauran kasashe su soki laifuffukan da suka aikata ba.

Wadannan ’yan siyasan kasashen yammacin duniya wadanda suke farin ciki da ganin an tada hankali a duniya, suna kara mara wa mista Morrison baya, to, abin da suke yi, suna kara sanya kasashen duniya su kara sanin laifuffukan da sojojin Australiya suka aikata a Afghanistan, sa’an nan suna gane laifuffukan da kasashensu suka aikata da kuma yadda suke nuna girman kai da yin fuska biyu a wasu fannoni. (Tasallah Yuan)

—  相关新闻  —

Not Found!(404)