Yau ranar 3 ga watan Disamban da muke ciki, rana ce ta musamman da Majalissar Dinkin Duniya ta kebe don jaddada bukatar kula da nakasassu na kasashe daban daban yadda ya kamata.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, a nashi bangaren, ya dade yana kokarin kula da mutane masu bukata ta musamman, inda ya kan zauna tare da su, da tambaya kan yanayin da suke ciki a fannonin ayyuka, da karatu, da kuma zaman rayuwa. Ya taba bayyana cewa, nakasassu suna fama da matsala sosai, don haka ya kamata a kara lura da su, da kokarin biyan bukatunsu. Wadannan hotuna sun nuna yadda shugaba Xi Jinping yake jinjina ga wasu nakasassu, da kokarin karfafa gwiwarsu. (Bello Wang)