Masu nazari daga kasar Faransa sun gano a kwanan baya cewa, akwai wata alaka a tsakanin shan abin sha mai cike da sukari da kuma barazanar kamuwa da ciwon sankara. Duk da shan ruwan 'ya'yan itatuwa da aka matse, akwai yiwuwar hakan zai kara fuskantar barazanar kamuwa da ciwon sankara. Don haka masu nazarin sun ba da shawarar cewa, ya fi kyau a rage shan abin sha mai cike da sukari, a kokarin kare lafiyarmu
Masu nazari daga jami’a ta 13 ta Paris a Faransa sun kaddamar da sakamakon nazarinsu a kwanan baya, inda suka yi karin bayani da cewa, sun gudanar da wani nazari kan baligai ‘yan kasar Faransa fiye da dubu 100 daga shekarar 2009 zuwa shekarar 2018. Lokacin da aka fara nazarin, wadannan mutane suna cikin koshin lafiya, matsakaicin shekarunsu sun kai 42 a duniya, kana kuma kashi 21 cikin kashi 100 daga cikin su maza ne, yayin da sauran kashi 79 cikin kashi 100 mata ne. An yi bincike kan yawan abin sha mai cike da sukari da suka sha, da kuma gano ko sun kamu da ciwon sankara a lokacin gudanar da nazarin.
Sakamakon nazarin ya shaida cewa, abubuwan sha masu cike da sukari da yawansa ya kai mililita 100 a ko wace rana, ya kara barazanar kamuwa da ciwon sankara da kashi 18 cikin kashi 100, musamman ma barazanar kamuwa da ciwon sankarar mama ta karu da kashi 22 cikin kashi 100. Duk da shan ruwan 'ya'yan itatuwa da aka matse, barazanar kan karu.
Amma nazarin bai gano alaka dake tsakanin abubuwan sha masu sinadarin da ke sa abinci zaki a maimakon sukari, da kuma barazanar kamuwa da ciwon sankara ba. Duk da haka masu nazarin sun yi nuni da cewa, watakila dalilin da ya sa haka shi ne domin mutane ba safai su kan sha irin wannan abin sha ba kullum.
Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, mai yiwuwa ne sukarin da ke cikin abin sha zai yi illa ga kibar da aka yi tsakanin kayan cikin dan Adam da kuma yawan sukarin da ke jinin dan Adam, ta yadda hakan zai iya kara barazanar kamuwa da ciwon sankara. Ban da haka kuma, abubuwan da ake karawa a cikin abin sha domin kare shi ko kara masa dadi su ma suna kawo illa ga lafiyar jama’a.
Masu nazarin na Faransa sun kara da cewa, sun gudanar da nazarinsu ne ta hanyar kallo ba tare da yin gwaje-gwaje ba. Akwai bukatar tabbatar da sakamakon nazarinsu ta hanyar yin nazarce-nazarce da yawa. Amma sakamakon nazarinsu ya tunatar da cewa, watakila kara sanya haraji kan sukari da kuma inganta sa ido kan tallar abin sha mai cike da sukari da sauran matakai za su taimaka wajen rage yawan masu kamuwa da ciwon sankara. (Tasallah Yuan)