Wasu masu nazari daga kasar Amurka sun kaddamar da sakamakon nazarinsu a kwanan baya, inda suka nuna cewa, watakila shan maganin Aspirin na dogon lokaci zai taimaka wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sankarar hanta da kwan mace.
A cikin nazari na farko da masu nazari daga asibitin Massachusetts na Amurka suka gudanar, sun tantance bayanan da suka tattara dangane da lafiyar mutane dubu 133 tun daga shekarun 1980, sun gano cewa, idan mutum ya sha maganin Aspirin a ko wane mako bisa shawarar likita, to, barazanar da ake fuskanta wajen kamuwa da ciwon sankarar hanta zai ragu da kashi 49 cikin kashi 100. Idan kuma aka dauki shekaru fiye da 5 ana shan maganin, to, barazanar za ta ragu da kashi 59 cikin kashi 100.
Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta yi nuni da cewa, Idan aka ci gaba da shan maganin Aspirin bisa shawarar likita, to, barazanar kamuwa da ciwon sankarar hanta tana raguwa. Amma idan an daina shan maganin, to, ba maganin ba zai yi wani tasiri ba, daga baya bayan shekaru 8, maganin bai amfana wa lafiyar mutane ba. Duk da haka, ban da maganin na Aspirin, sauran nau’o’in magungunan kau da kumburi bai taimaka wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sankarar hanta ba.
A cikin nazari na biyu da masu nazari daga jami’ar Harvard ta Amurka suka gudanar, sun yi nazari kan bayanan da suka shafi mata fiye da dubu 200, ciki had da wasu 1054 da suka kamu da ciwon sankarar kwan mace. Masu nazarin sun gano cewa, in an kwatanta su da wadanda ba su taba shan maganin na Aspirin ba, barazanar kamuwa da ciwon sankarar kwan mace da matan da suka sha maganin kadan bisa shawarar likita a ko wace rana, suke fuskanta ta ragu da kashi 23 cikin kashi 100. Amma idan an sha da yawa, to, maganin bai amfana wa lafiyarsu ba.
Haka zalika ban da maganin na Aspirin, mai yiwuwa ne shan sauran nau’o’in magungunan kau da kumburi na dogon lokaci zai kara barazanar kamuwa da ciwon sankarar kwan mace. (Tasallah Yuan)