Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho a jiya, da takwaransa na Somalia, Ahmed IsseAwad.
Wang Yi, ya ce kasar Sin na daya daga cikin kasashe na farko da suka amince da ‘yancin kan Somalia, kuma ita ce kasa ta farko a gabashin Afrika da ta kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin.
Ya ce cikin shekarun da suka gabata, kasashen biyu sun mutunta juna bisa adalci da fahimta, haka kuma, sun rika goyon bayan juna kan batutuwan da suka shafi muradun kowannensu.
Ministan na kasar Sin, ya ce a shirye kasarsa take, ta hada hannu da Somalia wajen bada taimakon kayayyaki da gaggauta horar da jami’an da ake bukata na wanzar da zaman lafiya da sake gina kasar, tare da kara hada gwiwa a fannonin aikin gona da kiwon kifi da kiwon lafiya da sauran wasu bangarori. Har ila yau, ya ce a shirye Sin take ta ci gaba da karfafawa kamfanoninta gwiwar zuba jari da kasuwanci a Somali da kuma taimakawa sake bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar.
A nasa bangaren, Ahmed IsseAwad, wanda shi ya kira takwaran nasa na kasar Sin, ya bayyana godiya ga irin taimakon da Sin ta dade tana ba Somalia. Ya ce kasarsa na bada muhimmanci ga raya huldarta da Sin, sannan tana goyon bayan manufar Kasar Sin daya tak a duniya, tare da adawa da ‘yancin kan Taiwan.
A cewarsa, a shirye Somalia take ta hada hannu da Sin wajen gudanar da jerin shirye-shirye domin bikin cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya a tsakaninsu da karfafa hadin gwiwa a fannin ginin ababen more rayuwa da al’adu da sauran bangarori, domin kara bunkasa huldar kasashen biyu. (Fa’iza Mustapha)