Yayin bikin cika shekaru 70 da sojojin Sin suka taimaka wa Koriya ta Arewa wajen turjewa zaluncin Amurka, Xi Jinping ya bayyana cewa, ba za a manta babbar gudummawar da tsoffin sojojin kasar suka bayar wajen kare zaman lafiyar sabuwar kasar Sin da aka kafa a lokacin da ma kasashen duniya ba. Kuma, ba za a manta da shahidan da suka rasa rayukansu cikin yakin taimaka wa Koriya ta Arewa turjewa zaluncin Amurka ba.
Shugaba Xi ya kuma gaida dukkanin tsoffin sojoji dake raye, da kuma nuna godiyarsa ga dukkanin masu goyon bayan zaman lafiyar kasa da kasa, a sa'i daya kuma, ya yaba matuka da zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasar Koriya ta Arewa. (Maryam)