Wakilin kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka wajen yakar ta'addanci a Syria

cri2020-08-28 10:00:06

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga kasashen duniya, da su taimaka wajen ganin an yaki ayyukan ta'addanci a kasar Syria.

Wakilin na kasar Sin ya kuma shaidawa MDD cewa, yanayin tsaro a kasar Syria yana bukatar kulawa ta musamman. A don haka ya kamata kasashen duniya, su ci gaba da taimakawa kasar, don ta yaki ayyukan ta'addanci, kamar yadda dokar kasa da kasa da kudurorin kwamitin tsaro na majalisar suka tanada.

Ya kuma shaidawa kwamitin sulhu na MDDr cewa, kungiyar IS tana kara kai hare-hare a kasar ta Syria. Inda a baya-bayan nan ma, wasu abubuwan fashewa da nakiyoyin da aka binne a karkashin kasa, suka haddasa mummunan barna. Kuma ana danganta gabilin abubuwa da dama dake faruwa a kasar, ga ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Ya ce, ayyukan yaki da ta'addanci ba abu ne da za a ga bayansa kwata-kwata ba, kuma aikin ne na dogon lokaci. A saboda haka,ya zama wajibi gamayyar kasa da kasa, ta kara sanya ido da daukar matakan yaki da ta'addanci na bai daya, ciki har da kasar Syria.

Yana mai cewa, bai kamata a kawar da ido game da abin da ke faruwa a kasar Syria ba. Tilas a hada karfi da karfe da kara taimakawa kasar, muddin ana fatan cimma wannan buri.(Ibrahim)

Not Found!(404)