Mataimakin zaunannen jakadan kasar Sin a MDD, Geng Shuang, ya ce dole ne a gaggauta warware rikicin siyasar Syria, yana mai nanata cewa, dole ne a gaggauta dage takunkuman da aka sanyawa kasar da yaki ya daidaita.
Yayin wani taro ta kafar bidiyo na kwamitin sulhu na MDD, kan yanayin siysar Syria, Geng Shuang, ya ce dole ne a gaggauta samar da maslaha a siyasance, domin ita ce hanya daya ta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a Syria. Ya kara da cewa, ya kamata bangarori masu ruwa da tsaki su shiga a dama da su cikin tattaunawar da ake yi karkashin kwamitin gyara kundin tsarin mulkin kasar.
Har ila yau, jakadan ya ce suna fatan ganin dukkan bangarorin sun yi kokarin samar da maslaha da wuri, wadda kuma za ta dace da yanayin kasar da kuma yin la'akari da bukatunsu. (Fa'iza Mustapha)