Mataimakiyar firaministan kasar Sin ta jaddada bukatar inganta kandagarki da magance cutar AIDS

cri2019-11-29 10:15:19

Mataimakiyar firaministan kasar Sin Sun Chunlan, ta jaddada bukatar inganta kandagarki, da magance yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki wato AIDS ko Sida, da ma sauran cututtuka da ka iya yaduwa tsakankanin al'umma. Sun ta yi wannan tsokaci ne a jiya Alhamis, yayin wani rangadin duba ayyuka da ta gudanar a nan birnin Beijing.

Jami'ar ta ce, akwai bukatar maida hankali ga tushen al'umma, da karfafa kwarewa ta gudanar da ayyuka a matakin al'ummu, don tabbatar da nasarar kare lafiyar jama'a.

Daga nan sai ta yi kira ga kananan hukumomin gwamnati, da su kara azama wajen aikin ba da kariya daga kamuwa da cutar AIDS, su inganta tsarin ba da hidima ga masu dauke da cutar, tare da amfani da kungiyoyin al'umma wajen fadakar da kowa, game da amfanin shiga wannan muhimmin aiki.

Sun ta kara da cewa, ya dace a shigar da aikin fadakar da jama'a cikin tsarin ilimin makarantu, ta yadda za a wayar da kan jama'a game da hanyoyin kare kai daga kamuwa da wannan cuta, da dabarun dakile yaduwar ta da ma magance ta. (Saminu)

404 Not Found

404 Not Found


nginx