A watan Disambar shekara ta 2015, a wajen taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka ko kuma FOCAC a takaice wanda aka yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanar da wasu muhimman shirye-shirye guda goma na karfafa hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wadanda suka shafi raya masana'antu, da zamanintar da ayyukan gona, inganta ababen more rayuwar jama'a, da hada-hadar kudi da sauransu. A yau, za mu gabatar muku da wani bayani dangane da yadda fasahohin kasar Sin na yaki da cutar zazzabin cizon sauro ko kuma malariya ke amfanawa jama'ar Afirka.
Bisa wani rahoton da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta fitar, a shekarar 2016, adadin mutanen da suka kamu da cutar malariya ya kai miliyan 216, wanda ya karu da miliyan biyar idan aka kwatanta da na shekara ta 2015. A shekara ta 2016, yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon cutar ya kai dubu 445, kana kuma kimanin kashi 90 bisa dari na jimillar yawan mutanen da suka kamu da cutar malariya gami da wadanda suka mutu sanadiyyar cutar, a Afirka suke.
Tun shekara ta 2007, tawagar yaki da cutar malariya ta jami'ar koyon likitancin gargajiya na kasar Sin dake Guangzhou ta fara gudanar da nazarin yaki da cutar bisa "shirin yaki da malariya na kasar Sin" a kasar Comoros. Shugaban cibiyar nazarin ilimin likita na yankuna masu zafi ta jami'ar koyon likitancin gargajiya ta kasar Sin dake Guangzhou, shehun malami Song Jianping ya bayyana cewa, "shirin yaki da malariya na kasar Sin" wani shiri ne mai amfani wanda ya hada dabarun kasar Sin da halin da ake ciki a kasashen Afirka. Song ya nuna cewa:
"Wata babbar matsala da Afirka ke fuskanta wajen yaki da cutar malariya ita ce rashin samun magani, abun da ya sa cutar ke kashe mutanen da ba su iya samun magani da jinya da wuri ba. Abu na biyu shi ne, matakan yaki da cutar ba su da kyau sosai. Na uku, dabarun magani gami da kashe sauro ba su taka rawa sosai ba wajen murkushe cutar malariya. Bayan shekara ta 2007, mun fara amfani da sinadarin artemisinin na kasar Sin a cikin wasu tsibirai uku na kasar Comoros, inda muka samar da wani nau'in maganin yaki da malariya mai kunshe da sinadarin artemisinin bisa likitancin gargajiya na kasar Sin. Shirin ya maida hankali kan murkushe asalin cutar malariya, domin kawar da cutar cikin sauri. A Comoros, mun samu sakamako mai gamsarwa, inda muka kawo karshen yaduwar cutar malariya cikin dan kankanin lokaci."
A shekara ta 2014, ba'a samu mutuwar mutane ba sakamakon cutar malariya a Comoros, kuma yawan mutanen da suka kamu da cutar ya ragu da kashi 98 bisa dari idan aka kwatanta da na shekara ta 2006. Comoros ta zama kasa ta farko a nahiyar Afirka wadda ta samu nasarar dakile yaduwar cutar malariya ta hanyar amfani da maganin kasar Sin. Game da dimbin nasarorin da aka samu, shehun malami Song Jianping ya bayyana cewa, aikin hana yaduwar cutar malariya a duk fadin duniya, wani aiki ne dake bukatar kokari da hadin-gwiwar bangarori dababn-daban, inda ya ce:
"A ganina, idan kasashen Afirka na son kawar da cutar malariya baki daya, ya zama dole su daura niyya, wato, ba ma kawai wadanda suka kamu da cutar su yi niyya ba, ita ma gwamnati ta daura niyyar ganin bayan cutar, don haka wani muhimmin dalilin da ya sa Comoros ta samu nasara shi ne cikakken goyon-baya daga gwamnatin kasar. Abu na biyu shi ne ya kamata a aiwatar da wani shirin da ya dace. Shirin kasar Sin, musamman ma shirin da muka aiwatar a Comoros, ya maida hankali kan shawo kan abin da haddasa cutar malariya, ta yadda a karshe muka iya kawar da cutar baki daya."
Baya ga kasar Comoros, maganin yaki da cutar malariya dake amfani da sinadarin artemisinin da "shirin yaki da cutar malariya na kasar Sin" suna taka rawar gani a sauran wasu kasashen Afirka da dama. Ministar kula da harkokin kiwon lafiya, da raya unguwanni, da jinsi, da tsoffi da yara ta kasar Tanzaniya, Ummy Ally Mwalimu ta ce, sakamakon taimakon da gwamnatin kasar Sin ta bayar, yawan mutanen da suka kamu da cutar malariya a kasarta na dada raguwa, kuma tana fatan Sin da Tanzaniya za su karfafa hadin-gwiwa a fannin kiwon lafiya, ta yadda jama'a za su kara cin moriya. Madam Ummy ta ce:
"Gwamnatin kasar Sin ta ba mu dimbin taimako. Kwararru daga kasar Sin sun yi kokari tare da takwarorinsu na Tanzaniya don gudanar da nazari kan cutar malariya da sauro, da lalubo bakin zaren daidaita matsalar. Ina farin-cikin ganin cewa, adadin mutanen da suka kamu da cutar ya ragu ainun, wato daga kashi 14 bisa dari a shekara ta 2012 zuwa kashi 7 bisa dari a shekara ta 2018. Muna iya cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu game da karfafa hadin-gwiwa tsakanin kwararrun kiwon lafiya na kasashen biyu wajen kawar da cutar malariya."(Murtala Zhang)