Masana kiwon lafiya daga kasashen Namibiya da Angola suna taro a wannan mako a garin Nkurenkuru dake shiyyar yammacin Kavango na kasar Namibiya domin tsara dabarun hadin gwiwa wajen kawar da cutar zazzabin malariya a kasashen biyu.
Mwalengwa Nghipumbwa, jami'in sanya ido kan shirin yaki da cutar malariya na ma'aikatar lafiya da ayyuka na musamman ta kasar Namibiya ya ce, manufar shirya wannan shirin ita ce, domin baiwa kasashen biyu kwarin gwiwa wajen yakar cutar ta malariya wacce ke bazuwa a sassan iyakokin kasashen biyu.
Wasu alkaluma da ma'aikatar kiwon lafiya da ayyukan na musamman ta fitar sun nuna cewa, an samu wadanda suka kamu da cutar malariyar a kasar Namibiya kimanin 24,000 tsakanin watannin Janairu zuwa Mayun wannan shekara.(Ahmad Fagam)