Kasar Sin za ta kokarta don kau da cutar malariya nan da shekarar 2020

cri2018-04-24 17:37:45

Ranar 26 ga wata za ta kasance ranar yaki da cutar malariya ta kasar Sin karo na 11. Mao Qun'an, shugaban hukumar kula da aikin rigakafin cutar malariya ta kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin ya bayyana a yau cewa, da ma ana yawan samun masu kamuwa da cutar malariya a kasar Sin, amma yanzu kasar ta kusan cimma burinta na kau da cutar kwata kwata. A cikin wannan sabon zamanin da ake ciki, za a mai da hankali kan aikin shawo kan cutar da za ta shigo daga ketare, a kokarin kau da cutar nan da shekarar 2020.(Kande Gao)

404 Not Found

404 Not Found


nginx/1.26.1