Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 16:01:28    
An tattauna kan batun kara hadin gwiwa a taron koli na kungiyar OIC

cri
A ran 9 ga wata, a birnin Istanbul na kasar Turkiya, an yi taron koli na kungiyar taron Musulunci wato OIC na yini daya. A yayin taron, an tattauna a game da kara hadin gwiwa da yin kokarin tinkarar kalubale kana tattalin arziki da dai sauransu.

Shugaban kasar Turkiya Abdullah Gul shi ya jagoranci taron, inda ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Musulunci su kara hada gwiwa, da aiwatar da tsarin samar da rangwame wajen yin cinikayya a tsakanin kasashen Musulunci, da kuma kara hada jari don yin cinikayya a tsakanin kasashen Musulunci.

Babban sakataren kungiyar OIC Ekmeleddin Ihsanoglu ya furta cewa, a shekarun baya, kungiyar ta kara yanayin cinikayyar dake tsakanin kasashen Musulunci ta hanyar aiwatar da tsarin samar da rangwame wajen yin cinikayya a tsakanin kasashen mambobi, kuma za ta dauki sauran mataki kamar tsarin samar da rangwame wajen biyan haraji da dai sauransu don ciyar da cinikayyar da ake yi a yankunan iyakar kasashe gaba.(Asabe)