Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 11:25:06    
Ofisoshin jakadancin Sin a kasashen Uganda da Kongo(kinshasa) sun shirya bukukuwan nune-nunen hotuna kan nasarorin da aka samu a gun taron tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika

cri
A ranar 9 ga wata, ofishin jakadancin Sin a kasar Uganda ya shirya bikin nune-nunen hotuna kan nasarorin da aka samu bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, minista mai kula da harkokin cikin gida a fannin cinikayya na kasar Uganda Wambuzi Gagawala da sauran manyan jami'an gwamnati da tawagogin Sin a kasar Uganda sun halarci wannan biki.

A cikin jawabin fatan alheri da mukaddashin ofishin jakadancin Sin a kasar Uganda Xu Jianguo ya yi, ya waiwayi nasarorin da kasar Uganda ta samu bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a shekara ta 2006, kuma ya bayyana ma'anar ziyarar firaministan Sin Wen Jiabao a gun taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunwar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da sabbin mataka 8 da za a dauka domin taimakawa kasashen Afrika.

Gagawala ya yaba wa goyon baya da gwamnatin Sin ke samarwa wajen aikin samun bunkasuwar tattalin arziki a kasar Uganda, kuma ya yi maraba da masu saka jari na Sin da su je kasar Uganda, domin sa kaimi ga kara kwarewar kasar Uganda, ta hakan, Uganda za ta ci gaba da samun kudin shiga daga kasashen waje.

Kana kuma, a wanna rana, ofishin jakadancin Sin a kasar Kongo(kinshasa) ya shirya bikin nune-nunen hotuna kan nasarorin da aka samu bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, an nuna hotuna kimanin 100 wajen bayyana sha'anin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannin aikin gona da ilmi da kiwon lafiya da dai sauran manyan ayyuka. Jami'an majalisar dokoki da na gwamnatin da manema labaru da dai sauran jama'a kimanin 100 sun halarci wajen wannan biki.(Bako)