Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 10:12:17    
Shugabannin kasashen Afrika sun darajanta hadin gwiwar da Sin da kasashen Afrika suke yi

cri
A ran 8 ga wata, a gun bikin bude taron ministoci na 4 na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika, shugabannin kasashe da yankuna da kungiyoyin Afrika sun yi jawabi domin nuna yabo ga dangantakar sada zumanci dake tsakanin Sin da kasashen Afrika, kuma sun darajanta ci gaban da kasashen Afrika da Sin suka samu bayan da aka yi taron koli na Beijing na dandalin, ban da wannan kuma, sun yi imani da cewa, matakan da Sin ta dauka wajen kara hada kai tsakanin bangarorin biyu, da kuma sabbin matakai 8 da Sin ta dauka na ba da taimako ga bunkasuwar kasashen Afrika, dukkansu za su taimakawa kasashen Afrika kan ayyukan bunkasuwa, bugu da kari, za su kara kaimi ga bunkasa dangantakar hadin gwiwa ta sada zumanci dake tsakanin bangarorin biyu.

Shugaban taron kuma shugaban kasar Massar Mr Muhammed Hosni Mubarak ya furta cewa, dandalin ya mayar da dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika a kan wani sabon matsayi, kuma ya ba da misali ta fuskar hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.

Mataimakin shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya fadi cewa, an kafa zumancin a tsakanin Sin da kasashen Afrika ne bisa tushen dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, kuma wannan dangantaka ce ta daidai wa daida.

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan Ahmed Al-Bashir ya nuna godiya ga kasa Sin a sakamakon goyon bayan da take bai wa kokarin da kasashe da yankuna da kuma kungiyoyin Afrika suke yi ta fuskar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankuna da kuma kokarin shawo kan rigingimun da ake yi a yankin.

Shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afrika Mr Jean Ping ya furta cewa, an kafa dangantakar hadin gwiwa ta sada zumanci bisa manyan tsare-tsare ne bisa tushen zumunci da hadin gwiwar jama'ar bangarorin biyu, kuma an kafa wannan zumunci ne yayin da kasar Sin ta nuna goyon baya ga ayyukan neman samun 'yancin kai na kasashen Afrika. Ko da yake, ana fuskantar matsalar hada-hadar kudi, Sin ta ci gaba da nuna goyon baya ga ayyukan bunkasuwar kasashen Afrika, kuma tana tsayawa tsayin daka kan cika alkawarin da ta yi wa kasashen Afrika. Dadin dadawa, kasar Sin ta ba da taimakonta ga ayyukan kiyaye zaman lafiya da ake yi a yankin Darfur na Sudan da kuma Somaliya, a sakamakon haka, ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afrika.

An labarta cewa, shugabannin kasashen Gabon da Uganda da Jamhuriyyar dimukradiyyar Kongo da Liberiya da Cote D'ivore da kuma Rwanda da dai sauransu su ma sun nuna kyakyawan fatan wajen bunkasa dangantakar dake tsakaninsu da Sin.(Amina)