Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 09:54:07    
Kamfanin CCECC ya ba da taimako ga kafa manyan ayyukan kasashen Afirka

cri
Alamu na ci gaba da nuna aminci tsakanin Sin da kasashen Afirka, inda daga kasar Algeriya dake arewacin Afirka zuwa kasar Botswana dake kudancin Afirka, daga kasar Tanzaniya dake gabashin Afirka zuwa kasar Nijeriya dake yammacin nahiyar, a ko ina za a iya ganin ma'aikatan kamfanin CCECC, wadanda suke taimakawa kasashen Afirka wajen gudanar da manyan ayyuka.

Mataimakin shugaban kamfanin CCECC Zhou Tianxiang ya bayyana cewa, a Nijeriya, kamfanin yana kafa hanyar jirgin kasa ta Abuja, tare da kara fadin tashar jiragen ruwa ta Apapa, da kafa wasu hanyoyi da gadoji da gidaje da dakunan motsa jiki. Bayan haka kuma, kamfanin yana kafa manyan ayyuka a kasashen Algeriya da Libya da Tanzaniya da Botswana da Uganda da Ruwanda da Djibouti. Mista Zhou ya furta cewa, kamfanin CCECC zai kammala duk wadannan ayyuka yadda ya kamata, a yunkurin samar da alheri ga jama'ar kasashen Afirka da ba da gudummawa ga samun hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.(Fatima)