Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 20:10:32    
An rufe taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka

cri

A ran 9 ga wata, a birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar, an rufe taron ministoci karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa. Ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi da ministan kasuwanci na kasar Chen Deming, da ministocin harkokin waje da ministoci da wakilai masu kula da hadin kan tattalin arziki na kasashen Afirka 49 sun halarci taron.

An mayar da "inganta dangantakar abokantaka ta sabon salo tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare domin neman samun dauwamammen ci gaba" a matsayin babban taken taron. Firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya halarci bikin bude taron da kuma sanar da sabbin matakai 8 da Sin za ta dauka don hadin gwiwa tare da Afirka. Yang Jiechi da Chen Deming sun bayar da rahoto kan yaya aka aiwatar da sakamkon da aka samu a yayin taron koli na Beijing. Wakilan kasashe daban daban da suka halarci taron sun darajanta ayyukan da aka gudanar bayan taron koli na Beijing da aka yi a shekara ta 2006, da kuma nuna yabo ga sabbin matakan da gwamnatin Sin za ta dauka don tallafawa Afirka. Suna ganin cewa, wannan ya nuna goyon baya da taimako da ko da yaushe kasar Sin ke nuna wa Afirka, wanda kuma zai samar da kyakkyawar makoma ta hadin kan Sin da Afirka. Haka kuma wakilan sun bayyana cewa, suna son hada kai tare da Sin domin aiwatar da matakai daban daban a tsanake, ta yadda za a iya ciyar da dangantakar abokantaka ta sabon salo a tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare tsare zuwa gaba.(Kande Gao)