Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 11:06:26    
Kasar Iran ta yi gaggarumin taron murnar ranar cika shekaru 30 da mamaye ofishin jakadanci na kasar Amurka

cri

A ran 4 ga wata, an yi gaggaruman tarurruka a yankuna da yawa na kasar Iran don murnar ranar cika shekaru 30 da mamaye ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar.

A birnin Tehran babban birnin kasar, duban mutane sun taru a tsohon ofishin jakadancin kasar Amurka da ke kasar Iran dake cibiyar birnin. Galibinsu sun rike da kyallaye da tutocin kasar Iran, kuma sun yi ikirarin nuna adawa da kasashen Amurka da Isra'ila don taya murnar mamaye ofishin jakadancin kasar Amurka dake Iran da tsare jami'an ofishin da daliban kasar suka yi a shekarar 1979. Tsohon shugaban majalisar dokoki ta kasar Iran Haddad Adel ya yi jawabi cewa, kasar Amurka ba ta dakatar da daukar manufar nuna adawa ga kasar Iran ba, amma kasar Iran ba za ta yi watsi da ikon yin amfani nukiliya ba a sakamakon matsin lamba da aka yi mata. Ya kuma jaddada cewa, mamaye ofishin jakadancin kasar Amurka gaskiya ne, sabo da kasar Amurka ta yi amfani da shi wajen yin aikin leken asiri.

Bugu da kari, a wannan rana, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayar da sanarwa kan wannan lamari cewa, kasar Amurka tana neman bunkasa huldar kawo moriyar juna da girmama juna tare da kasar Iran, kuma tana fatan gwamnatin Iran za ta yi hangen nesa da sauke nauyin dake kanta don kyautata huldarta da gamayyar kasa da kasa ciki har da kasar Amurka.(Lami)