Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 09:56:50    
Ministan harkokin musamman na kasar Nijeriya ya yi kira da a kara hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika

cri
Wakilinmu ya ruwaito mana labari cewa, a ran 2 ga wata, ministan harkokin musamman na kasar Nijeriya Ibrahim Musa Kazaure wanda ya halarci dandalin kula da hakkin dan Adam na Beijing na 2, ya shedawa wakilinmu cewa, kasashen Afrika suna fatan za su kara hada kai da kasar Sin.

Ibrahim Musa Kazaure ya yi wannan furuci ne yayin da ya tabo taron ministoci na 4 na dandalin hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da za a yi a Sharm el Sheikh na kasar Massar, inda ya ce, shugabannin Sin da kasashen Afrika sun tattauna kan matsalolin da kasashen Afrika suke fuskanta ta fuskar bunkasuwa da dai sauransu. Shugabannin kasashen Afrika za su bayyana abubuwan da suke yin tsammani a dandalin ta yadda za su kara hada kai da kasar Sin.

An habarta cewa, Ibrahim Musa Kazaure ya nuna kyakyawan fata ga taron ministoci na 4 na dandalin hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da za a yi nan baga, kuma yana fatan za a kara wangar da hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika.(amina)