Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-15 09:13:21    
Shugaban kasar Nijeriya ya ce, an riga an maido da zaman lafiya a yankin Nijer Delta

cri
A ran 14 ga wata a birnin Abuja, shugaban kasar Nijeiya Umaru Yar'Adua ya bayyana cewa, an riga an kawo karshen rikice-rikicen da suka faru a muhimmin yankin samar da man fetur na kasar wato yankin Nijer Delta, lokacin zaman lafiya ya zo.

Yar'Adua ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da sakataren kungiyar OPEC Abdulla El-Badri dake ziyara a kasar a wannan rana. Yar'Adua ya furta cewa, wani umurnin yin ahuwa da ya gabatar ya mai da dakaru da yawa sun ajiye makamai da maido da zaman lafiya a yankin Nijer Delta, yanzu dai gwamnatin tana gudanar da ayyukan da bangarorin daban daban da abin ya shafa suke shiga bayan da aka gabatar da umurnin yin ahuwa.

An fara gudanar da umurnin yin ahuwa da shugaba Yar'Adua ya gabatar a ran 6 ga watan Agusta, kuma an kammala shi a ran 4 ga wata, a lokacin wasu dakaru fiye da dubu 8 sun samu ahuwa bayan sun ajiye makamai.(Zainab)