Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-30 11:10:52    
Ban Ki-moon da wakilan dindindin nakasashe daban daban a MDD suna taya murnar cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin

cri

A ran 29 ga wata da dare, zaunannen jakadan Sin dake MDD Zhang Yesui da uwar gidansa Chen Naiqing sun shirya wata liyafa don taya murar cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin. Mutane 500, ciki har da babban sakataren MDD Ban Ki-moon, da shugaban babban taron MDD a karo na 64 Ali Treki da jakadun kasashe daban-daban dake MDD, da kuma ma'aikatan ketare daga MDD, har da shugabannin Sinawa 'yan kaka-gida dake zaune a yankunan gabashin kasar Amurka.

Ban Ki-moon ya yi fatan alheri don taya murnar cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin. Ya ce, kasar Sin wata muhimmiyar mamba ce ta MDD. Kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da harkokin majalisar. Shugaban Sin Hu Jintao ya halarci tarurukan koli guda 3 na MDD, inda ya yi muhimmin jawabi. Ban Ki-moon ya yi fatan samun dorewar wadata ga kasar Sin tare da begenta da ta kara taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na duniya.

A daren wannan rana, a gun liyafar, an kuma nuna hotuna, wadanda suka bayyana nasarorin da kasar Sin ta samu cikin shekaru 60 da suka gabata. Baki da suka halarci wajen liyafar sun yi yabo sosai kan manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu da kuma na zamantakewar al'umma, kana sun darajta muhimmiyar rawa da kasar Sin take takawa a cikin al'amuran MDD.(amina)